Zuma ya bayyana cewa, kasarsa ta ji dadi da ganin samun babban ci gaba kan ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito da kuma hadin gwiwar kasashen biyu. Kasar Afirka ta Kudu tana son kara yin mu'amala tare da kasar Sin a fannoni daban daban a MDD da kungiyar BRICS ciki har da fannin tsaron kasa, kana za su yi kokarin bada gudummawa wajen tabbatar da tsaro a nahiyar Afirka har ma a duniya baki daya.
A nasa bangare, janar Chang Wanquan ya ce, kasar Afirka ta Kudu ta kasance mai muhimmaci a nahiyar Afirka har ma da duniya, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Afirka ta Kudu wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kansu, da inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi, da kara yin hadin gwiwarsu a fannin kiyaye tsaron kasa don bada gudummawa ga jama'arsu da yankuna tare da tabbatar da zaman lafiya da wadata a duniya gaba daya. (Zainab)