in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin nune-nunen kayayyakin kasar Afirka ta Kudu na shekarar 2014 a birnin Beijing
2014-10-31 15:41:22 cri
An kaddamar da bikin nune-nunen kayayyakin kasar Afirka ta Kudu na shekarar 2014 a jiya Alhamis 30 ga wata a nan birnin Beijing.

A gun bikin budewar, mataimakin ministan harkokin ciniki na kasar Sin Fang Aiqing ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance kasar wadda Afirka ta Kudu ta fi yawan fitar mata da kayayyaki har na tsawon shekaru biyar a jere, kana kasar Afirka ta Kudu ta kasance wadda kasar Sin ta fi yin ciniki da zuba mata jari tsakanin kasashen Afirka har na tsawon shekaru hudu a jere. A halin yanzu, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen biyu ya fadada daga hakar ma'adinai, da kayayyakin gine-gine zuwa makamashi na bola-jari, motoci, watsa labaru, samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya da dai sauransu. Kuma yana fatan bikin nune-nunen kayayyakin kasar Afirka ta Kudu zai kasance dandalin yin mu'amala a tsakanin bangarorin masana'antu da ciniki na kasashen biyu. An bude kasuwar kasar Sin ga kasashen duniya, kuma tana fatan kamfanonin kasar Afirka ta Kudu za su yi amfani da wannan dama.

A nasa bangare, ministan harkokin ciniki da masana'antu na kasar Afirka ta Kudu Rob Davies ya bayyana cewa, cikin kayayyakin kirar kasar Afirka ta Kudu da aka sayar da su a nan kasar Sin, wadanda suka kunshi karin daraja da fasahohi masu ci gaba ba su wuce kashi 7% ba . Ta hanyar wannan bikin nune-nunen, za a fadada hadin gwiwa tare da kasar Sin a wannan fanni, kana yana fatan kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin fasahohin aikin gona, fasahar zamani da dai sauransu. Kuma kasar Afirka ta Kudu za ta kara kyautata yanayin zuba jari a kasar don amfanawa kamfanonin kasashen waje, haka kuma za ta bullo da wasu manufofin sassauta biyan haraji ga kamfanonin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China