Kasar Afrika ta Kudu za ta karbi bakuncin babban taron kasa da kasa na shekara shekara karo na 35 na Crime Stoppers International CSI wato laifuffukan da ke sabawa dokokin kasa da kasa, wanda za'a gudanar a karon farko a wata kasar dake nahiyar Afrika, a cewar masu shirya taron.
Wannan dandali da aka tsai da shiryawa daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Oktoba a birnin Cap na da manufar baiwa mahalarta damar yin tsinkaye da nazari daga dukkan fannoni kan manyan laifuffukan kasa da kasa, da kuma bullo da hanyoyin da za su taimaka wajen yaki da wannan annoba. (Maman Ada)