A ranar 1 ga watan nan ne aka bude taron sauyin yanayi na MDD a birnin Lima na kasar Peru.
Jim kadan da bude taron mataimakin shugaban tawagar kasar Sin, kuma wakilin musamman na kasar Sin kan shawarwari game da sauyin yanayi Su Wei, ya bayyana cewa babban jigo a wannan karo shi ne tabbatar da ayyukan da za a yi, ya kuma yi fatan kasashe masu wadata zasu cika alkawarin da suka yi domin sa kaimi ga a samun ci gaba a taron.
Su Wei ya kuwa ce, kamar a kullu, muhimmin batu da za a tattauna a wannan karo shi ne, matakan da ya dace a dauka wajen tinkarar sauyin yanayi, wadanda suka kasu kashi biyu. Wato na farko, kara tabbatar da matakan da kasashen duniya za su dauka wajen tinkarar sauyin yanayin kafin shekarar 2020. Sai kuwa, tattaunawa kan ayyuka, da matakan da kasahen duniya za su dauka bayan shekarar 2020, domin inganta karfin tinkarar kalubalen na sauyin yanayi. (Amina)