in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jaddada niyyarta wajen yaki da sauyin yanayi
2014-09-24 09:50:54 cri

Kasar Sin ta jaddada a ranar Talata niyyarta ta yaki da sauyin yanayi, tare da kuma daukar matakin bunkasa dangantakar kudu da kudu wajen fuskantar wannan bazarana ga duniya.

Da yake jawabi a yayin babban taron MDD kan yanayi a matsayinsa na manzon musammun na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mataimakin faraminista Zhang Gaoli ya nuna cewa, kasar Sin za ta sanar da wasu ayyuka na ganin shekarar 2020 kan canjin yanayi a daidai lokacin da ya dace, ayyukan da za su kai ga samun cigaba mai tasiri a wajen kokarin rage yawan iska ta dumama yanayi, da kara yin amfani da makamashin da ba irin na man fetur ba, da kuma kara yawan gandunan daji.

Kasar Sin za ta kuma rubanya taimakon kudin shekara domin tallafawa kafa wani asusun dangantakar kudu da kudu, ta yadda za a fuskantar sauyin yanayi daga bakin shekara mai zuwa, kana za ta samar da dalar Amurka miliyan shida a shekara mai zuwa domin taimakawa sakatare janar na MDD kyautata dangantakar kudu da kudu a wannan bangare, in ji mista Zhang. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China