Mataimakin faraministan kasar Sin, Zhang Gaoli ya bayyana a ranar Litinin a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, kasar Sin za ta ba da dalar Amurka miliyan shida domin tallafawa kokarin da sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ke yi na bunkasa dangantakar Kudu-Kudu kan sauyin yanayi.
Mista Zhang, dake halartar taron MDD kan sauyin yanayi a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wadannan kalamai a yayin wani zaman taro tare da mista Ban, wanda ya nuna yabo kan kokarin da kasar Sin take, da kuma muhimman ayyukan da ta gudanar a wajen yaki da wannan barazanar duniya.
Gabanin taron nasu, shugabannin biyu sun halarci wani bikin wanda a yayinsa kasar Sin ta baiwa MDD kyautar wani rukunin bayanai kan shingen kariyar duniya, domin taimakawa gamayyar kasa da kasa fuskantar kalubalolin sauyin yanayi. (Maman Ada)