Shugaban tagawar kasar Sin a taron sauyin yanayi na MDD, kuma mataimakin direktan kwamitin yin kwaskwarima, da raya kasar Sin Mr Xie Zhenhua, ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashe masu wadata su cika alkawuran da suka yi, na samar da kudade ga asusun tinkarar sauyin yanayi na kasa da kasa. A cewarsa, wannan mataki ya kasance mihimmin batu a taron na wannan karo.
A gun babban taron yanayin da aka gudanar a ran 20 ga wata nan bisa matakin manyan jami'ai, Xie Zhenhua ya furta cewa, samar da kudaden gudanarwa ya kasance wani muhimmin mataki ga taron na birnin Warsaw.
Har ila yau Mr. Xie ya kara da cewa hakan ya kasance tushe da kuma sharadi ga ayyukan da kasashe masu tasowa za su yi, ciki hadda rage gurbataccen hayakin dake jawo dumamar yanayi, da kara karfinsu domin rage tasirin da sauyin yanayi ke kawowa. Baya ga musanyar dabarun kimiya da fasaha, da aikin raya karfin tinkarar sauyin yanayin, da gudanar da irin wannan aiki a fili da sauransu.
Ya ce rashin isashen kudi, zai haifar da matsala a fannin amincewa da tsarin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.
Bisa kudurin da aka fitar a baya bayan nan, an bayyana cewa ya kamata, kasashe masu wadata su samar da kudade da ya kai dala biliyan 30, daga shekarar 2010 zuwa ta 2012, domin kaddamar da asusun kiyaye muhalli, su kuma samar da kimanin dala biliyan 100 a kowace shekara, daga shekarar 2013 zuwa ta 2020, domin taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi yadda ya kamata, sai dai kawo yanzu ba a tattara isassun kudin da ake fatan samarwa ba tukuna. (Amina)