Kasar Sin ta bayyana fatarta ta ganin a cimma matsaya a kan sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi da za'a fitar a karshen shekara mai zuwa ta 2015, in ji babban mai shiga tsakani a kan yanayi na kasar Xie Zhenhua a ranar Talatan nan.
Mr. Xie ya sanar da hakan ne sakamakon babban taron a kan sauyin yanayi da MDD ta kira na yini daya, da zummar hada wani kuduri da za'a cimma domin samar da wata yarjejeniya a kan sauyin yanayi da za'a rattaba hannu a birnin Paris na kasar Faransa shekara mai zuwa.
Mr. Xie wanda shi ne mataimakin shugaba a kwamitin ci gaban kasar da kwaskwarima ya ce, kasar Sin za ta taka rawarta yadda ya kamata wajen tabbata da cimma nasasar wannan kuduri daga dukkan bangarori.
Yana mai lura da cewa, kasar tana tsaye a kan hanya yadda ya kamata na ganin ta cika alkawarinta na rage yawan sinadarin carbon mai gurbata muhalli da kashi 40 zuwa 45 a cikin 100 nan da shekara ta 2020. Ya yi bayanin cewa, daga matsayin da take na 2005, adadin sinadarin carbon ya ragu da kashi 28.5 a cikin 100 wanda ya nuna kwatankwacin tan biliyan 2.5 a kan yadda take fitarwa. (Fatimah)