Ranar 22 zuwa 23 ga wata, Zhang Gaoli, mataimakin firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Amurka da na Faransa da wasu shugabannin kasashen waje da kuma uwar gidan sarkin kasar Holland, wadanda suka halarci taron koli na MDD kan sauyin yanayi a birnin New York na kasar Amurka.
Yayin da Mista Zhang yake ganawa da shugaba Barack Obama na Amurka, ya ce, shugaba Xi Jinping na kasar Sin yana maraba da mista Obama da ya halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar yin hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific wato APEC da za a yi a watan Nuwamban bana a birnin Beijing tare da kawo ziyara a kasar Sin ziyara. Kasar Sin na son ci gaba da yin kokari tare da Amurka, a kokarin mayar da tinkarar sauyin yanayi cikin hadin gwiwa tamkar wani sabon fanni na raya dangantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Amurka. Har wa yau wajibi ne bangarorin 2 su tsaya tsayin daka kan sauke nauyi tare bisa bambancin da ke kasancewa a a tsakaninsu, su inganta tuntubar juna da yin mu'amala da juna, su girmama tsarin daidaita batutuwa a tsakanin sassa daban daban, a kokarin ba da gudummawa wajen daidaita sauyin yanayi tare.
A nasa bangaren kuma, mista Obama ya ce, kasarsa na sa muhimmanci kan inganta hadin gwiwa da kasar Sin a fannin tinkarar sauyin yanayi, tare da fatan samun ci-gaba a fannoni daban daba.(Tasallah)