Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, a jiya Lahadi ya yi marhabin da wani rahoto na masana a kan canjin yanayi, a inda ya bukaci daukacin kasashen duniya, da su dauki matakan da suka dace. Wata sanarwar kakakin babban sakataren na MDD, ta ce, Ban Ki-moon ya bukaci dukanin kasashe da su gaggauta daukar matakan da suka dace a game da canjin yanayi, domin a yi tinkaho da gagarumar nasara kafin taron koli da za'a yi a kan canjin yanayi a birnin New York ta Amurka a ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 2014 da muke ciki.
Sanarwar ta bukaci kasashen da su dauki duk matakan da suka dace na kaiwa ga cimma yarjejeniya a kan yanayi a bisa wani tsari na shari'a a shekara ta 2015.
Shi dai wannan rahoto wanda kwararru suka gabatar a kan canjin yanayi mai shafuna 33, ya samu tofa albarkacin masana har 1,250, kuma ya samu amincewa na gwamnatoci 194.
Shi dai wannan rahoto, ana sa rai zai yi jagora ga dukanin kasashe wadanda suka yi alkawari za su cimma wata yarjejeniya nan da shekara ta 2015, a kokarin da ake na hana dumamar yanayi na duniya kaiwa wani mataki da zai kawo barazana ta yin lahani ga duniyar. (Suwaiba)