in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ai daga kasashen Afrika 22 na samun horo kan sauyin yanayi
2013-12-11 12:23:57 cri

Kimanin wakilan gwamnatoci daga kasashen Afrika 22 ke halartar wani taron kara wa juna sani kan matakan yaki da illar da sauyin yanayi ke kawo wa muhallin halittun ruwan teku tun ranar Talata a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire.

Horon na kwanaki uku na da manufar kara azama daga wajen gwamnatoci kan wajabcin aiwatar da matakan kula da muhalli da na wuraren jama'a domin taimakawa rage illar sauye-sauyen yanayi, a cewar shugabannin wannan taro.

Hukumar kula da muhalli ta MDD ta dauki nauyin shirya wannan dandali da ya tattara wakilai daga shiyyar da ta shafi yarjejeniyar Abidjan, yankin da ya taso tun daga kasar Mauritaniya ta gabar bakin ruwan Afrika har zuwa kudanci.

Taron dai kuma zai taimaka wajen kara ilmi, karfafa kwarewa da samar da matakan aiki game da sauyin yanayi ga mahalarta taron, ta yadda za su aiwatar da su bisa tushen wani tsarin dake tafiya tare da kare muhalli. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China