A ranar Lahadin nan 21 ga wata a birnin New York, cibiyar MDD, babban magatakardar majalissar Ban Ki-moon ya sanar da cewa, babu wani sabon shiri na yaki da sauyin yanayi, yana mai kira ga kasashe da su daidaita wannan lamari da kansu.
Ban Ki-moon ya ce, wannan duniya da ake ciki ita ce ake fatan zuri'an masu zuwa su zauna a ciki, don haka babu wani sabon shiri tun da ba a da wata sabuwar duniya, a bayanin da ya yi wa manema labarai bayan aiki da kusan mutane da aka kiyasta sun kai 300,000 da suke zanga-zanga a karkashin wata cibiyar mai aiki kan batun sauyin yanayi a birnin New York.
Mr. Ban wanda shi ma ya saka rigar wannan kungiya da aka rubuta "ni ma ina son daukan mataki game da sauyin yanayi", ya yi tafiya na 'dan wani lokaci a kasa tare da tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Al Gore, magajin garin New York Bill De Blasio, da kuma ministan yanayi na kasar Faransa Segolene Royal.
Wannan tafiya a kasa dai ana ganin ita ce mafi girma da aka taba yi a kasar Amurka domin nuna bukatar a dauki mataki da zai kawo ci gaba ga sauyin yanayi na duniya.
A wajen birnin na New York kuma, daga birnin Landan zuwa Bogota, wadansu mutane kimanin 270,000 suka fito a bukukuwa 2,500 da aka yi a fadin duniya baki daya kamar yadda masu shirya taron suka bayyana.
Wannan taro dai, an yi shi ne kwanaki biyu kafin Mr. Ban ya bude babban taron game da sauyin yanayi a cibiyar majalissar dinkin duniyar dake birnin New York wanda ake sa ran zai samu halartar shugabannin kasashe da gwamnatoci 120.
A lokacin wannan taro, ana sa ran tsai da matsaya game da babban taron da za'a yi a birnin Paris na kasar Faransa a watan Disambar shekara mai zuwa ta 2015 da nufin cimma matsaya na karshe kan kundin sauyin yanayi na duniya baki daya. (Fatimah)