in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nasarar taron sauyin yanayi na Warsaw ya danganta da burin kasashe masu wadata
2013-11-11 15:29:10 cri

Yau Litinin 11 ga wata ne, aka kira taro karo na 19 na kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD kuma taro karo na 9 na yarjejeniyar Kyoto a Warsaw, hedkwatar kasar Poland.

An bayar da rahoton cewa, kudurin farko na yarjejeniyar Kyato, zai kare ne a karshen shekarar 2012 yayin da shekarar 2013 zuwa 2020 zai kasance mataki na biyu na yarjejeniyar, alkawarin da kasashe daban-daban za su yi wajen rage fitar da gurbatattun abubuwa zai jawo hankalin kasa da kasa a taron.

Wani muhimmin abu na daban a taron shi ne kudi da fasaha. Kasa da kasa sun cimma matsaya daya a taron Doha a shekarar da ta gabata, inda aka kayyade cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2015, ya kamata kasashe masu wadata su samar da kudi a kalla dala biliyan 30 domin kafa asusun kiyaye muhalli, ta yadda za a taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi. Amma har yanzu, ba a tabbatar da wadannan kudade ba. Ko za a cimma nasarar shawarwari a wannan shekara ko sai a nan gaba ko a'a, hakan ya danganta da burin kasashe masu wadata a siyasance wato ko za su cika alkawarinsu ko a'a. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China