in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya bukaci a yi kudi ga sinadari mai gurbata muhalli
2014-09-23 10:31:16 cri

A ranar Litinin din nan bankin duniya ya ce, gwamnatocin kasashe 73 da yankuna 11 tare da kamfanoni fiye da 1,000 sun bayyana goyon bayansu ga yin kudi ga sinadari mai gurbata muhalli kafin babban taro a kan sauyin yanayi na MDD.

Wadannan kasashe da yankuna da suka hada da Sin, Rasha, tarayyar Turai, Indonesia, Mexico da Afrika ta Kudu suke da alhakin kashi 54 a cikin 100 na fitar da iskan gas mai gurbata muhalli na duniya baki daya.

Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ya fadi a cikin wata sanarwa cewa, gwamnatoci masu wakiltar kusan rabin al'ummar duniya, kuma kashi 52 a cikin 100 na GDPn duniya baki daya sun nuna goyon bayansu a kan a yi kudi a kan adadin iska mai gurbata muhalli a matsayin wani abun da ya kamata, in ko da kuwa ba zai gamsar ba, a matsayin wani mataki na magance matsalar sauyin yanayi, da kuma wani mataki na ci gaba a kokarin rage makamashi mai gurbata muhalli. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China