in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron sauyin yanayi na MDD a birnin Lima
2014-12-02 16:04:00 cri

An bude taron masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 20, kuma taron wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar Kyoto karo na 10 a birnin Lima hedkwatar kasar Peru.

Taron wanda aka bude a ranar 1 ga watan nan, ya samu halartar jami'ai da za su tattauna kan yadda za a tinkari al'amuran sauyin yanayi cikin kwanaki 12.

Yayin jawabinsa na bude taron, ministan muhallin kasar Peru Manuel Pulgar-Vidal wanda ke jagorantar zaman na wannan lokaci, ya bayyana kyakkyawan fatansa game da cimma yarjejeya mai amfani a ya yin taron wadda za ta bada damar sassauta halin da ake ciki game da sauyin yanayi.

Kaza lika ya yi kira ga bangarorin daban-daban da su kara hada kai da juna wajen kyautata tunani cikin adalci da daidaito, tare kuma da daukar matakai masu ma'ana, ta yadda taron zai zama wani dandali na sauraro, da fadin bukatun bangarori daban-daban.

Za a kammala taron ne dai na wannan karo a ranar 12 ga wata, wanda kuma ya samu halartar wakilai kimanin 190, ciki hadda jami'an kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, da masana, da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu.

A ganin wasu manazarta, taron na wannan karo ya kasance muhimmin kashi cikin shawarwarin dake gudana tsakanin bangarori daban-daban kan batun sauyin yanayi, wanda kuma zai kawo babban alfanu ga auna yiwuwar cimma sabuwar yarjejeniyar yanayi a shekarar 2015 a birnin Paris. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China