in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro na MDD ya yi allah wadai da wani harin kunar bakin wake da aka kai a wata makaranta a Nigeria
2014-11-11 16:40:42 cri
Kwamitin tsaro na MDD ya yi kakkausar suka a game da harin kunar bakin wake da aka kai a wata makarantar gwamnati a Potiskum wanda ke arewa maso gabashin Nigeria.

Wata majiya daga asibitin jihar, tace harin ya haifar da asarar rayukan dalibai 78, inda kuma wasu yara daliban 45 suka samu raunuka.

Kwamitin tsaro na MDD ya fada a cikin wata sanarwa da aka baiwa manema labarai cewar ya kamata duk wadanda ke da hannu cikin wannan aika-aikar a Nigeriya da kasar waje su fuskanci tsarin doka.

Kwamitin tsaron na MDD. ya bayyana matukar alhini da jaje ga iyalan daliban, kuma a daidai lokaci guda kwamitin ya nuna amincewarsa da kokarin da gwamnatin Nigeriya ke yi wajen samar da kariya ga makarantu da kuma daliban makaranta da kuma kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da taimako da kuma gwagwarmayar tabbatar da cewar wadanda ke aikata wadannan munanan laifukan sun fuskanci shari'a.

Kawo yanzu babu wata kungiya data dauki alhakin aiwatar da wannan harin da aka kai da bam, ko da yake mazauna jihar ta Yobe sun dora laifin wannan harin a kan kungiyar 'yan tsageran Boko Haram masu tada kayar baya, wadanda dama suke da alhakin aiwatar da kashe-kashen jama'a a Nigeria tun daga shekarar 2009.(Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China