Bisa labarin da gidan telebijin na Al Jazeera na kasar Qatar ya bayar, an ce boma-boman sun fashe ne a jiya Talata da misalin karfe 11 na rana bisa lokacin wurin, bayan da wata mace ta tashi bam din dake jikinta cikin dandazon jama'a. Jim kadan da hakan ne kuma wata macen daban ita ma ta tarwatsa kanta, a kusa da inda bam din na farko ya tashi.
Sai dai majiyar kamfanin dillancin labaru ta AFP ta ce mutane 45 ne harin bom din ya hallaka.
Bayan aukuwar hare-haren biyu an ga motocin jami'an bada agajin gaggawa na garzayawa wurin da lamarin ya auku. Inda suka rika kai mutanen da suka ji raunika zuwa asibitin dake kusa da wurin, yayin da dakarun rundunar soji ke kula da asibitin.
Wani da ya shaida yadda lamarin ya auku, ya ce akwai matukar cunkoson marasa lafiya a asibitin, sakamakon yawan wadanda suka jikkata a wannan lamari.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kaddamr da hare-haren. (Zainab)