Jirgin da kamfanin kera jiragen ruwa na CSIC wato China Shipbuilding Industry Corporation an mika shi ne ga kasar Nigeriya a birnin Qidong, dake lardin Jiangsu na gabashim kasar Sin.
Jirgin mai tsawon mita 95.5 da fadin mita 12.2 yana iya fitar da ruwa da ya kai tan 1,800, abinda ya sa zai zama mafi girma kuma mai dauke da kayan zamani cikin jiragen ruwan tsaron teku da Nigeriya ke da su a yanzu,in ji kamfanin na CSIC.
Wannan jirgin za'a yi aiki da shi wajen tabbatar da tsaro akan tekun kasar, sa ido da lura da rijiyoyin man da kasar ke da su, sannan kuma za'a yi amfani da shi wajen ayyukan da ya shafi kamun kifi, bada ceto da dai sauran su.