in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan aikin gina layin dogo a Najeriya ya bunkasa tattalain arzikin kasar
2014-11-23 16:41:23 cri
Masharhanta na fatan cewa, aikin gina layin dogo da zai lakume biliyoyin daloli a Najeriya wanda aka sanya hannu a makon da ya gabata tsakanin gwamnatin kasar ta Najeriya da wani kamfanin kasar Sin wato CRCC da zai gudanar da aikin, zai samar da wata dama da bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Aikin gina layin dogon da zai lashe tsabar kudi dala biliyan 11.97 ya kasance kwangila mafi girma da kamfanin ya samu a wata kasar waje.kuma zai kai tsawon kilomita 1,402, inda zai hade cibiyar kasuwancin kasar wato Lagos dake yammacin kasar da kuma garin Kalaba da ke gabashin kasar

Bugu da kari ana saran aikin zai samar da guraben aikin yi 200,000 sannan za a kara samar da wasu guraben aikin na din-din-din da zarar layin ya fara aiki.

Har ila wannan aiki zai kara samar da dama ga ci gaban tattalin arzikin jihohin da layin zai ratsa su da kuma Najeriya baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China