Kaza lika, bayan harin da dakarun suka kai garin, 'yan sandan kasar sun kwashe sa'o'i hudu suna yin musayar wuta da dakarun, inda 'yan sanda suka yi amfani da jirgin saman leken asiri. Ya zuwa yanzu, hukumar kula da harkokin cikin gidan kasar ta Kenya ta sanar da mutuwar mutane 48, kana bisa bayanan 'yan sanda, sun ce, watakila adadin wadanda suka mutu na iya karuwa. (Maryam)