in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Kenya sun kashe mutane 5 da aka zargi da kai hari a yankin Lamu
2014-06-20 10:58:00 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Kenya da rundunar sojojin tsaron kasar sun tabbatar a ranar 19 ga wata, cewa an harbe mutane 5 har lahira da aka zarginsu da kai hari a garin Mpeketoni dake yankin Lamu na kasar yayin da sojojin kasar suke kokarin cafke su.

Wani jami'in kasar ya bayyana cewa, sojojin kasar Kenya sun yi musayar wuta tare da dakaru 5 da aka zarginsu da kai hari a yankin Lamu a shiyyar Bochai dake garin Mpeketoni, kuma sun harbe wadannan mutane biyar har lahira.

Babban jami'in 'yan sanda na yankin Lamu Samuel Obara ya ce, sun riga sun kara jibge 'yan sanda a yankin kan iyaka da Somaliya, da kara yin sintiri domin dakile duk wani yunkurin kai wasu sabbin hare-hare a wannan yankin. Kana 'yan sandan wurin na cigaba da yin hadin gwiwa tare da sojojin kasar Kenya don tabbatar da tsaro a kan iyaka da Somaliya.

Bisa kididdigar da gwamnatin kasar Kenya ta yi, an ce, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon harin da aka kai garin Mpeketoni a ranar 15 da 16 ga wata ya zarce 60. Maharan sun kona bankuna da kantuna, a yayin da kuma iyalai suka rasa gidaje kimanin 500. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China