Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya la'anci farmakin da aka kai a yankin Ramu na kasar Kenya. Cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar Mr. Ban ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon hari, da gwamnatin kasar ta Kenya, tare da fatan wadanda suka samu raunuka za su samu sauki cikin hanzari.
Kaza lika babban magatakardar MDD ya sake jaddada cewa, majalissar na goyon bayan gwamnatin kasar Kenya, da jama'arta a yakin da suke yi da ta'addanci. Ya kuma yi imanin cewa hukumomi a kasar za su yi iyakacin kokari, wajen hukunta wadancan suka aikata wannan ta'asa. (Bilkisu)