in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi kasar Amurka ta koyi fasahohi daga Sin a fannin hadin gwiwa da kasashen Afirka
2014-06-06 14:10:17 cri
Wani sharhi da Jaridar Business Day ta kasar Kenya ta yi a kwanan baya, ya nuna cewa, kamata ya yi Amurka ta yi koyi da fasahohin kasar Sin, a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da kasashen Afirka.

Sharhin ya ci gaba da cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka, da firaministan kasar Sin sun ziyarci nahiyar Afirka a watan Mayun da ya shude, duk kuwa da cewa kasashen biyu suna da hanyoyi mabanbanta na yin hadin gwiwa da kasashen Afirka.

Yayin da kasar Amurka ke mai da hankali kan wanzuwar zaman lafiya da tsaro, musamman yaki da ta'addanci da 'yan fashin teku, da kuma rikicin cikin gida na Sudan ta Kudu, da na jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya. A hannu guda Sin na dora muhimmanci kan ba da gudummawa, da zuba jari, da hadin gwiwa da kasashen Afirka. Baya ga batun samar da rancen kudi ga nahiyar domin aiwatar da ayyukan raya kasa, da zuba jari a fannonin makamashi da na ayyukan more rayuwa, da kuma tallafawa bunkasuwar tattalin arzikin Afirka a nan gaba.

Haka zalika, sharhin ya nuna cewa, tsaro da bunkasuwar tattalin arziki dukkansu suna da muhimmaci ga nahiyar Afirka. Kuma a matsayin manyan kasashen duniya, ya kamata Sin da Amurka su lura da wadannan fannoni baki daya. A shekaru da dama da suka gabata, kasar Amurka ba ta yi ciniki da hadin gwiwa da dama a kasashen Afirka, kana ba ta aiwatar da shirin ciniki da shirin samar da wutar lantarki a Afirka yadda ya kamata ba da shugaban kasar Barack Obama ya gabatar, yayin da ya kai ziyara a nahiyar Afirka a shekarar 2013.

A nata bangaren yayin da kasar Sin ke hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da kasashen Afirka, a sa'i guda ta ba da gudummawa a fannin kiyaye tsaron nahiyar, ta amfani da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, da na yaki da 'yan fashin teku. Don haka sharhin ke ganin kamata ya yi kasar Amurka ta tsara wasu matakai masu inganci na sa kaimi ga yin ciniki da zuba jari a Afirka, da kuma nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen samun bunkasuwar tattalin arziki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China