A cewar babban manajan kamfanin Wang Jinyu, kasancewar Kenya kasar dake da kasuwa mai armashi ga nau'o'in ababen hawa daban daban, ya sa suka ga dacewar gabatar da sabbin motocin, a matsayin hanyar bunkasa harkokin sufuri a kasar da ma nahiyar Afirka baki daya.
A jawabinsa yayin kaddamar da wannan sabuwar mota ta kamfanin na Foton, magatakardar kwamitin JKS na birnin Beijing Guo Jinlong, cewa ya yi bisa la'akari da matsayin Kenya a nahiyar Afirka, jarin da wannan kamfanin na Sin ya zuwa a kasar, ya nuna fadadar alaka tsakanin Sin da kasashen nahiyar ta fuskar cinikayya.
Ya zuwa yanzu dai kamfanin na Foton ya zuba jarin da ya kai dalar Amurka miliyan 30, a sashensa na hada motoci cikin kasar ta Kenya, baya ga wasu rassan da yake da su a Kenyan da kuma kasar Uganda. (Saminu Alhassan)