Bisa labarin da kafofin yada labaru na wurin suka bayar, an ce, an kai wannan hari ne a yankin Polomok, kusa da garin Mpeketoni. Baki daya hare-haren biyu sun haddasa mutuwar mutane 65. Kuma kungiyar Islama ta Al-Shabaab ta Somaliya ta riga ta sanar da daukar alharin kai wadannan hare-hare. (Fatima Liu)