Kwamitin sulhun MDD ya ba da sanarwa a ran 19 ga wata, inda ya yi kakkausar suka ga harin da aka kaiwa wurin ibadar Yahudawa a birnin Kudus.
Kwamitin ya kuma karawa shugabanni da jama'ar Palasdinu da Isra'ila kwarin gwiwar hada kai da juna, domin sassauta halin da suke ciki, da hana amfani da karfin tuwo, da kaucewa duk wani mataki na takala, da fatan cimma burin wanzar da zaman lafiya cikin hadin gwiwa.
Idan ba a manta ba dai, an kai harin a ranar 18 ga wata ne a wani wurin ibada na Yahudawa, lamarin da ya haifar da rasuwar Yahudawa 4, yayin da kuma 'yan sandan Isra'ila suka harbe wadanda suka kai farmakin su biyu. (Amina)