in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya nuna damuwarsa game da rashin cimma matsayar tsagaita bude wuta tsakanin Palasdinu da Isra'ila
2014-08-09 17:00:30 cri
Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ta bakin kakakinsa ya ba da wata sanarwa a ran 8 ga wata cewa, Mr Ban yana bakin ciki sosai saboda Palasdinu da Isra'ila ba su kai ga matsaya daya wajen tsawaita wa'adin yarjejeniyar hana jin karar makamai tsakaninsu ba, kuma karin fararen hulan da suka mutu cikin rikicin ya bata masa da rai sosai. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta ba da wata sanarwar yin kira ga bangarorin biyu da su daina bude wuta tsakainsu da komawa teburin shawarwari. Ban da haka kuma, kungiyar agajin duniya ta Red Cross ta yi tir da matakin da bangarorin biyu suka dauka na keta dokar jin kai ta kasa da kasa. Haka kuma, asusun taimakawa kananan yara na MDD ya ba da rahoto cewa, kananan yara a kalla 447 sun mutu sakamakon rikicin zirin Gaza.

Haka kuma, Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da rokokin da aka harba zuwa Isra'ila, tare da kalubalantar bangarori daban-daban da su fitar da wani tsarin tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, da cimma yarjejeniyar hana jin karar makamai tsakaninsu a birnin Alkahira na kasar ta Masar. A ganinsa, tsawaita wa'adin yarjejeniyar hana bude wuta tsakanin bangarorin biyu na da muhimmanci sosai wajen sa kaimi ga cimma nasarar shawarwari da magance wasu matsaloli masu zurfi tsakaninsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China