in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta dage haramcin kamun kifi na wani lokaci a Gaza
2014-08-18 15:00:22 cri
Wani jami'in Isra'ila ya sanar da cewa, kasar ta Isra'ila ta dage haramcin kamun kifi na dan wani lokaci da ta kakaba wa yankin Gaza, inda a wannan karon mazauna yankin za su rika kamun kifi a wasu gabar ruwayen Gaza.

Jami'in wanda ya shaidawa jaridar Ha'aretz da ke fito wa a kowace rana, wannan wani karamci ne da zai kai ga cimma wata yarjejeniyar da za ta kawo karshen hare-haren da Isra'ila ta fara kai wa a yankin na Gaza tun a ranar 8 ga watan Yuli, yayin da masu shiga tsakanin Palasdinawa da Isra'ila ke tattaunawa a birnin Alkahira na kasar Masar.

A ranar Lahadi ne firaministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu ya bayyana cewa,ba za cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude ta din-din-din ba,idan har ba a biya bukatun tsaron Isra'ila ba. Na farko Isra'ila ta bukaci da a janye sojoji a zirin Gaza kana a kwance damarar makaman Hamas, lamarin da Hamas din ta ce ba zai yiwu ba.

Bugu da kari Isra'ila na da niyyar sassauta kangiyar da ta yiwa zirin na Gaza, amma tana bukatar hukumar Palasdinawa da ta karbi ikon kula da zirga-zirgar kan iyakan na Gaza kana Isra'ila ta bayar da taimakon farfado da yankin.

A yau Litinin ne yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'I 120 da aka cimma tsakanin sassan biyu ke kare wa, kuma har yanzu babu tabbas ko za a kara tsawaita ta ko a'a, yayin da aka ci gaba da yin fada a makonni biyu da suka gabata lokacin da wa'adin ya kare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China