in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta yanke shawarar daina shawarwari da Palasdinu
2014-04-25 20:47:38 cri

Ofishin firaministan Isra'ila ya ba da wata sanarwa a ran 24 ga wata cewa, Isra'ila ta yanke shawarar dakatar da shawarwari tare da Palasdinu kan batun shimfida zaman lafiya.

Sanarwar kuma ta bayyana cewa, Isra'ila ba za ta yi shawarwari tare da gwamnatin Palasdinu dakungiyar Hamas ke mara mata baya ba ko kadan. Ta ce, Hamas wata kungiya ce ta ta'addanci dake da burin hallaka Isra'ila. Haka kuma, sanarwar ta cigaba da cewa, Isra'ila za ta dauki matakai a jere domin mayar da martani.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira wani taron ministoci a wannan rana, domin tattauna matakan da Isra'ila za ta dauka bayan da Hamas da Fatah suka hade wuri guda. A cikin wata sanarwar da ya bayar bayan taron, Benjamin Netanyahu ya ce, shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya daddale yarjejeniyar jituwa tare da Hamas yayin da Isra'ila take kokarin yin shawarwarin shimfida zaman lafiya da ita, lamarin da ya nuna cewa, Palasdinu ba ta da nufin ci gaba da shawarwari tare da Isra'ila. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China