in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Palasdinu ya yi kira da a tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2014-08-05 20:47:21 cri
Shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya maraba da shirin hana jin karar makamai na tsawon awo'i 72 a zirin Gaza a ran talata 5 ga wata, tare da yin kira ga Isra'ila da ta tabbatar da hakan.

Bisa labarin da kafar yada labaru ta Palasdinu ta bayar, an ce, Abbas yayi maraba da yarjejeniyar hana bude wuta wadda ta fara aiki tun daga karfe 8 na safe a ran 5 ga wata bisa lokacin wurin. Sannan ya yi kira ga Isra'ila da ta amince da hakan, ya kuma kalubalance ta da ta yarda da shawarar da Masar ta bayar na hana jin karar makamai a zirin Gaza har abada.

Kazalika, jami'in musamman mai kula da harkokin jin kai na MDD Navi Pillay ta ba da sanarwa a Geneva a ran 5 ga wata, inda da kakkausar murya ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kaiwa fararen hula a zirin Gaza. A cewar ta, ya kamata a kiyaye masu aikin jin kai da na'urorin ba da taimako a cikin rikici bisa dokar jin kai na kasa da kasa. Hukumar ba da taimako ga 'yan gudun hijira Palasdinawa ta MDD UNRWA ta mai da wasu makarantu a zirin Gaza matsayin mafaka na wucin gadi domin karbar 'yan gudun hijira dake fama da hare-haren bom da sojin Isra'ila suke kai.

A nata bangare kuma, Madam Pillay ta ce, hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai wa makarantun MDD shida, sun yi sanadin rasa rayukan kananan yara da fararen hula da dama. Don haka harin da aka kai ma makarantu da masu aikin ceto laifi ne dake taka dokar jin kai ta kasa da kasa, akwai yiwuwa zai kasance aikata laifin yaki. Ban da haka kuma, madam Pillay ta yi tir da harin da sojin Isra'ila suka kaiwa asibitoci a Gaza. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China