in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na maraba da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Palasdinu
2014-08-28 16:29:14 cri

Bangarorin al'ummar Palasdinu da na Isra'ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 26 ga watan nan, matakin da kasashe da hukumomin duniya da dama suka nuna matukar gamsuwa da shi, ciki hadda Rasha, da Amurka, da kawancen kasashen Turai, da MDD da sauransu.

Karkashin wannan zarafi dai ana fatan fidda wata manufa ta warware matsalar dake addabar bangarorin biyu cikin dogon lokaci.

Game da hakan ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da sanarwa a jiya Laraba, tana mai kira ga bangarorin biyu da su aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma yadda ya kamata, su kuma fidda manufar samun daidaito wajen warware batun zirin Gaza ba tare da wani bata lokaci ba.

Kazalika, ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya fidda wata sanarwa a ranar 26 ga wata, yana mai bayyana matukar fatansa na ci gaba da daina kaiwa juna hari tsakanin bangarorin biyu. Har ila yau sanarwar ta kuma bukaci da a dauki matakai da suka dace, wajen tabbatar da samarwa fararen hula dake zirin Gaza tallafin jin kai.

Dadin dadawa, kwamitin EU ya ba da tasa sanarwa a ranar 26 ga watan nan, wadda yake bayyan cewa, sai dai sake gudanar da yunkurin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya, ka iya wanzar da kwanciyar hankali ga Palasdinawa da tsagin Isra'ila a nan gaba.

A daya bangaren kuma ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya ba da sanarwar nanata muhimmancin dake akwai wajen farfado da batun warware rikicin dake addabar sassan biyu a siyasance, tare kuma da nuna fatan sanya himma da gwazo wajen gudanar da shawarwari karkashin shiga tsakanin kasar Masar, domin dai kaiwa ga cimma wata manufa mai dorewa.

Ban da haka kuma, babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ya gabatar da wata sanarwa a wannan rana, inda ya yi kira ga bangarorin biyu da su koma teburin shawarwari, domin kaiwa ga cimma matsaya daya game da matsayinsu na karshe. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China