in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falesdinu ta ki yarda da yarjejeniyar da Amurka ta gabatar game da yin shawarwarin zaman lafiya a tsakaninta da Isra'ila
2014-01-04 16:41:55 cri
Ranar 2 ga wata, ofishin firaministan kasar Isra'ila ya ba da wata sanarwar cewa, a wannan rana, John Kerry, sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya sake ziyartar kasar tare da yin shawarwari da firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Kafin shawarwarin, Mr. Kerry ya ba da sanarwar cewa, idan Falesdinu da Isra'ila sun yi kokari tare, akwai yiwuwar samun zaman lafiya a tsakaninsu.

Amma a wannan rana, kwamitin tsakiya na kungiyar Fatah ya furta cewa, Falesdinu ta ki yarda da yarjejeniyar da Mr. Kerry ya gabatar, ciki had da jibge sojoji a gabar yammacin kogin Jordan. Ta kuma furta cewa, ziyarar Mr. Kerry a Falesdinu ba za ta samu ci gaba ba, kuma Falesdinu ba za ta yarda da shirinsa na zaman lafiya ba.

Wata majiya ta fayyace cewa, yarjejeniyar da Mr. Kerry ya gabatar ta hada da amincewa da kasancewar sojojin Isra'ila a kasar Falaesdinu da za a kafa a nan gaba, lamarin da a ganin Falesdinu, Amurka tana yunkurin kiyaye moriyar Isra'ila ne, don haka Falasdinu ta ki yarda da yarjejeniyar. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China