Ministan harkokin cikin gidan kasar Ukraine ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, daga nata bangare kasar Ukraine ta yanke shawarar tabbatar da iyakar yankin ta da kasar Rasha, kuma gwamnatin ta samu iznin tabbatar da hakan.
Ofishin watsa labaru ta hukumar tsaron iyakar kasa ta Ukraine ta tabbatar da cewa, yanzu haka ana jiran umurnin shugaban kasar dangane da wannan batu, domin tabbatar da ikon hukumomin daban-daban na gwamnati kan aikin tabbatar da shata iyakar kasa.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, shi ma ya furta cewa, Rasha za ta ci gaba da sa kaimi ga warware batun Ukraine bisa yarjejeniyar da aka kulla a Minsk. Ya kuma yi kira ga mahukuntan Ukraine da su ci gaba da shawarwari da yankunan gabashin kasar, don cimma wata yarjejeniya da za ta samu amincewar bangarorin biyu. (Amina)