Tattaunawar da bangarori uku masu ruwa da tsaki game da rikicin kasar Ukraine ta kammala ba tare da cimma matsaya ba.
Bangarorin dai da suka hada da kungiyar hadin gwiwa a fannin harajin kwastan ta kasashen Rasha, da Belarus da Kazakhstan, da kuma kungiyar tarayyar Turai da kasar Ukraine, sun tashi taronsu na jiya Talata ne a birnin Minsk hedkwatar Belarus, ba tare da cimma wata nasara ba.
Cikin manyan jami'an da suka halarci taron dai akwai shugaban kasar Belarus Alexander Grigoryevich Lukashenko, da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, da na Kazakstan Nursultan Nazarbayev da kuma na Ukraine Petro Poroshenko. Kaza lika babbar jami'a mai kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro ta EU Madam Catherine Ashton ita ma ta halarci wannan taro.
Yayin ganawarsa da 'yan jaridu bayan kammalar taron, mai masaukin baki Alexander Grigoryevich Lukashenko ya ce an yi iyakacin kokari wajen warware rikicin kasar ta Ukraine, sai dai hakan ta ci tura sakamakon sarkakiyar da al'amura suka yi a Ukraine.
Ya kuma ce mahalartan taron sun yarda da batun daukar matakan sassauta hargitsin dake addabar kasar, da sakin mutane da ake tsare da su, baya ga warware batun 'yan gudun hijira da na bada tallafin jin kai.
A nasa bangare, shugaba Putin ya bayyana cewa, Rasha na mutunta zabin al'umma da ikonsu na mulkin kai, tare da mutunta ayyukan siyasarta, kana ba za ta hana kasa da kasa da su kulla kawance ta fannin aikin soja ko tattalin arziki ba, sai dai fa a sa'i guda tana fatan matakin da za a dauka ba zai dakushe moriyar sauran kasashe ba.
Kaza lika, Petro Poroshenko ya ce matakin da Ukraine ke dauka game da warware rikicin dake addabar kasar na da matukar amfani, kana dinkewar kasar itace hanya daya tilo da za ta kawo karshen zubar da jini, da ba da tabbaci ga farfadowar gabashin kasar bayan rikicin dake aukuwa yanzu haka.
Bugu da kari a cewarsa kokarin neman shiga EU da Ukraine ke yi, ba zai kawo wata illa ga sauran kasashe mambobin kungiyar ba ta fannin harajin kwastan, maimakon hakan, zai ma bunkasa harkokin cinikayya cikin 'yanci tsakaninsu. (Amina)