in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori biyu masu gwagwarmaya da juna a Ukraine sun zargi juna da laifin saba yarjejejniyar tsagaita bude wuta
2014-09-08 16:52:39 cri

Ranar 7 ga wata, gwamnatin kasar Ukraine da dakarun da ke gabashin kasar sun zargi juna da laifin saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma kai wa juna hare-hare, amma duk da haka za su ci gaba da martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakaninsu.

Dangane da lamarin, Vladimir Dzabarov, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasa da kasa na majalisar dattijai ta kasar Rasha kuma shugaban kwamitin wucin gadi da ke sa ido kan halin da ake ciki a Ukraine ya bayyana a wannan rana cewa, dukkan bangarorin 2 masu gwagwarmaya da juna a gabashin Ukraine suna martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, amma wasu masu dauke da makamai sun yi harbe-harbe. Ya yi fatan cewa, sojojin gwamnatin Ukraine da dakarun da ke gabashin kasar za su kai zuciya nesa, su kaucewa ta da tsokana a tsakaninsu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China