Kafin hakan shi ma shugaban majalisar wakilan kasar Sergey Naryshikin, ya bayyana cewa takunkumin da aka ce an kakabawa kasar ta Rasha ba shi da wata ma'ana ta fannin dokoki, sai dai zai iya haifar da hasara ga sassan biyu sakamakon tasirin sa a fannonin siyasa da tattalin arziki.
A ranar Litinin ne dai ministocin harkokin wajen kasashen Macedonia da Serbia suka bayyana cewa, kasashensu na neman shiga kungiyar EU, amma duk da haka ba za su shiga aikin kungiyar na sanyawa Rasha takunkumi ba. Har wa yau wakilan kasashen biyu sun ce bisa la'akari da moriyar su ta fuskar tattalin arzikinsu, ba za su goyi bayan takunkumi kan Rasha ba.
A wani ci gaban kuma, hukumar gudanar da ayyuka a kasashen waje ta kungiyar EU, ta zargi kasar Rasha da jigilar kayayyakin jin kai zuwa kasar Ukraine a karo na biyu, aikin da a cewar hukumar ya sabawa doka. Hukumar wadda ta bayyana hakan ta wata sanarwa, ta ce kasar Ukraine ba ta samu damar bincika ko amincewa da kayan da Rashan ta shigar ba, wanda hakan ya saba wa ka'idojin jin kai na kasa da kasa, ya kuma haifar da illa ga cikakken ikon yankin kasar da na mulkin kan Ukraine.
Hakan kuwa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zanta ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaban kwamitin kungiyar EU Jose Manuel Barroso daya bayan daya, game da yarjejeniyar da aka cimma a taron ministocin Rasha, da EU da Ukraine a ranar 12 ga watan nan, inda aka jinkirta lokacin fara aiwatar da yarjejeniyar da Ukraine da kasashe mambobin EU suka cimma zuwa ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2016. Yayin wannan zantawa dai shugaba Putin da Merkel sun nuna gamsuwa ga daukar wannan mataki.
Kana game da jinkirta lokacin fara aiwatar da yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tsakanin EU da Ukraine zuwa karshen shekarar mai zuwa, Mr. Putin da Barroso a yayin zantawar sun yi hasashen cewa, kamata ya yi a aiwatar da yarjejeniyar, a yayin da kuma shugaba Putin ke da ra'ayin cewa bai kamata a canja tsarin ciniki tsakanin Rasha da Ukraine ba. (Zainab)