Kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai ya fidda wata sanarwa a ran 29 ga wata cewa, inda ya nuna cewa, shugaban kwamitin Jose Manuel Durao Barroso ya yi shawarwari da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho don nuna damuwarsa kan yanayin da kasar Ukraine take ciki a halin yanzu.
Haka kuma, bisa labarin da fadar White House ta bayar a ran 29 ga wata, an ce, shugaban kasar Barack Obama zai kai ziyarar aiki a kasashen Turai cikin mako mai zuwa da kuma halartar taron koli na kungiyar yarjejeniyar Atlantic ta Arewa ta NATO. Babban direktan kula da harkokin Turai na kwamitin tsaron kasar Amurka Charles Kupchan ya bayyana cewa, yayin wannan ziyara, shugaba Obama zai yi tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa kan kara wa kasar Rasha takunkumi ta yadda za a tilasta mata neman hanyar siyasa don warware rikici, haka kuma a yayin taron, bangarorin da abin ya shafa za su karfafa taimakon siyasa da na tsaro ga kasar Ukraine. (Maryam)