Ana fatan shawarar da shugaban Rasha ya bayar za ta shimfida sharadi mai kyau ga warware rikicin Ukraine
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya shedawa manema labaru a ran 4 ga wata cewa, yana fatan shawarar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gabatar za ta shimfidar wani sharadi mai kyau wajen warware rikicin Ukraine a siyasance.
Yayin da ya amsa tambaya da manema labaru suka gabatar masa kan kiran da Putin yi na tsagaita bude wuta a gabashin Ukraine, Mr Qin ya ce, an lura da cewa shugaba Putin ya gabatar da shawarar warware rikicin Ukraine a siyasance, yana fatan wannan shawara za ta kawo amfani kan lamarin. (Amina)