in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana sakamakon zabe a Donetsk da Luhansk
2014-11-04 11:03:46 cri
Hukumomin zabe a "Jamhuriyyar Donetsk" da "Jamhuriyyar Luhansk" masu da'awar cin gashin kan su, sun gabatar da sakamakon zaben shugabanni da na majalisun dokokinsu a ranar 3 ga wata.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Ukraine suka bayar, an ce, hukumomin zabe a "kasashen biyu" sun gabatar da sunan Alexander Zakharchenko a matsayin wanda zai zama sabon firaministan Jamhuriyyar Donetsk, bayan da suka ce ya samu kuri'u kashi 78.9 cikin dari. Sai kuma firaministan "Jamhuriyyar Luhansk" Igor Plotnitsky, wanda shi ma ya lashe zaben shugabacin jamhuriyyar da kuri'u kaso 63.4 cikin dari.

Haka zalika kuma, "Jamhuriyyar Donetsk" da "Jamhuriyyar Luhansk" sun bayar da hadaddiyar sanarwa a daren ranar 3 ga watan, dake cewa suna fatan yin shawarwari tare da gwamnatin kasar Ukraine a karkashin sharadi gudanar da adalci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China