A cewar ministan tsaron bisa yarjejeniyar da kasar Ukraine ta kulla da wasu sauran kasashen duniya, a yayin taron koli na kungiyar tsaron NATO ne Ukraine din ta fara karbar tallafin makaman. Sai dai Geletei bai bayyana irin makaman da kasarsa ta karba ba. Koda yake ya ce Ukraine din na matukar bukatar makamai a halin yanzu.
Ya ce ta hanyar amfani da makaman ne dakarun sojin gwamnatin kasar za su iya kaiwa ga lalubo wuraren da 'yan adawar kasar suka boye makamansu tare da kai farmaki irin wadannan wurare.
A daya bangaren kuma sakataren shugaban jam'iyyar Regional ta kasar Boris Kolesnikov, ya ce ba za su shiga zaben majalisar dokokin kasar da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba ba. Mr. Kolesnikov ya bayyana cewa, kwamitin siyasa na jam'iyyar ya tsaida kuduri hakan ne, duba da yake-yake dake aukuwa a kasar, da kuma halin gaza gudanar da zabe a yankuna 44 na kasar. Kana ya jaddada cewa, a irin wannan hali na karuwar tashe-tashen hankula, da yawan kasha-kashen rayukan al'umma a kasar, zaben zai iya haifar da rarrabuwar kai a kasar. (Zainab)