in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD, Rasha da kungiyar NATO suna maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka daddale a Ukraine
2014-09-06 16:22:35 cri
Bangarori 3 na Ukraine, da kungiyar tsaron kasashen Turai, da kuma Rasha, gami da wakilan dakarun dake gabashin kasar Ukraine, sun sa hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta, a Minsk, fadar mulkin kasar Belarus, a ranar Jumma'a 5 ga wata. Daga bisani, shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ba da umarni ga sojojin kasar sa na dakatar da bude wuta a gabashin kasar. Haka kuma tsohon shugaban kasar Leonid Kuchma ya sanar a Jumma'a cewa, bangarorin dake arangama da juna a kasar Ukraine za su kafa wata kungiyar hadin gwiwa kafin ranar 8 mai zuwa, wadda za ta kula da aikin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Haka a nasu bangare, MDD, da Rasha, da kunigyar tsaro ta NATO, sun nuna marhabin ga yarjejeniyar da aka daddale a wannan karo.

Manyan jami'an da suka halarci taron da aka kira a Jumma'a 5 ga wata, sun hada da tsohon shugaban kasar Ukraine, Leonid Kuchma, da jakadan kasar Rasha dake Ukraine, da wakilin kungiyar tsaron kasashen Turai, gami da shugabannin dakarun sa kai masu adawa da gwamnatin kasar Ukraine.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China