Bangarorin biyu da ricikin Ukraine ya shafa sun amince da janye sojojinsu bisa tsawon kilomita 15 daga yankin rikici
Bangarorin uku da batun kasar Ukraine ya shafa da ke hada da kasar Ukraine, kungiyar tsaro ta Turai da kasar Rasha sun kulla wata yarjejeniya tare da wakilan dakarun gabashin kasar Ukraine a ran 19 ga wata a babban birnin kasar Belarus, Minsk, inda aka tsara cewa, ya kamata bangarorin biyu da rikicin Ukraine ya shafa sun amince da janye sojojinsu bisa tsawon kilomita 15 daga yankin rikici, don ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a ran 5 ga wata.
Haka kuma, yarjejeniyar da aka cimma a ran 19 ga wata na nuna cewa, ya kamata bangarorin biyu da rikicin ya shafa su dakatar da yin amfani da makamai, da kuma dakatar da kai wa juna hare-hare, da hana ajiye kayayyakin makamai a wuraren da fararen hulan kasar suke zaune, da hana kai hare-haren boma-bomai a yankin, sannan a fara kawar da shingayen da suka toshe hanyoyi, a janye sojojin ketare dake taimakawa dakarun gabashin Ukraine da kuma sojojin gwamnatin kasar Ukraine, da kuma sauran batutuwan da suka jibanci wannan rikicin. (Maryam)