A Talata ranar 2 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta bayyana cewa, Rasha ta fito fili tana kai hare-hare ga kasar Ukraine.
Game da zargin da kasar Ukraine ta yi, kasar Rasha ta bayyana cewa, babu wani sojin kasarta da ya shiga rikicin dake faruwa a kasar Ukraine. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana a gun taron manema labaru a ranar 2 ga wata cewa, yana fatan kasar Amurka za ta shawo kan kasar Ukraine ta yadda za a warware rikicin kasar ta hanyar siyasa.
Ministan harkokin wajen kasar Italiya kana mai jiran gadon sabon babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin diflomasiya da manufofin tsaro Federica Mogherini ya bayyana a birnin Brussels a ranar 2 ga wata cewa, kungiyar EU za ta tsai da sabon kuduri kan sanya wa kasar Rasha takunkumi kafin ranar 5 ga wata. (Zainab)