Kaza lika shugaba Putin ya jaddada cewa, kamata ya yi kungiyar tsaro da hadin gwiwar kasashen Turai ta sanya ido game da aiwatar da wannan tsarin.
Putin ya yi zanta da shugaba Poroshenko ne dai game da ci gaban da ake samu, game da taimakon jin kai da kasarsa ke bayarwa a Ukraine, kana sun yi musayar ra'ayi kan tasirin da hakan zai yi ga kawancen biya kudin kwastan na bai daya, idan kasar Ukraine ta zama mambar dake da alaka da kungiyar tarayyar kasashen Turai.
A wani ci gaba kuma, ofishin yada labarai na shugaban kasar Ukraine ya fidda wata sanarwa, dake cewa shugaban kasar da takwaransa na Rasha, sun tattauna game da hanyoyin da suka dace a bi, domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta dindindin a kudancin kasar Ukraine, kuma shugabannin biyu za su ci gaba da gudanar da shawarwari kan wannan batu. (Maryam)