in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Rasha ya yi kira da a dakatar da abin da ke faruwa a gabashin kasar Ukraine
2014-09-01 10:57:15 cri

Mataimakin kwamandan sojojin saman kasar Rasha Alexei Ragozin ya bayyana a ranar 31 ga watan Agusta cewa, dukkan sojojin saman kasar Rasha da aka kama su a gabashin kasar Ukraine sun koma gida.

Mr. Ragozin ya tabbatar da cewa, kasar Ukraine ta mika wa Rasha sojojin saman 10 ta da aka kama bayan da suka shiga kasar Ukraine ba tare da izni ba, yayin da itama kasar Rasha ta mika wa Ukaraine nata sojojin 63 da suka shiga kasar Rasha.

Hakazalika, dakarun fararen hula na Donetsk dake gabashin kasar Ukraine sun sanar da sakin sojojin kasar fiye da 200 da suke garkuwa da su.

A wannan rana, shugaban kasar Rasha Vładimir Putin ya bayyana fatan kasar Ukraine za ta hanzarta dakatar da hare-haren da ke kaiwa a gabashin kasar, kana ya zama tilas a yi shawarwari kan batun matsayin gabashin kasar Ukraine, da nufin tabbatar da kiyaye moriyar jama'ar yankin kudu maso gabashin kasar ta Ukraine ba tare da wani sharadi ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China