Yayin ziyarar wadda ita ce ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kai kasar cikin shekaru gwammai ana saran zai tattauna da takwaransa na kasar Sri Lanka Mahinda Rajapaksa da firaministan kasar D.M. Jayaratne da shugaban majalisar dokokin kasar Chamal Rajapaksa kan yadda za a bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a nan gaba.
Bugu da kari yayin wannan ziyara mai tarihi, ana saran kara bunkasa yankin tattalin arziki na hanyar siliki da kuma hanyar siliki ta kan teku cikin karni na 21,yayin da kasar ta Sri Lanka ta nuna goyon baya ga shirye-shiryen biyu da Sin ta gabatar.
Kasar ta Sri Lanka dai ita ce zango na uku na rangadin da shugaba Xi ya kai zuwa kasashe hudu na Asiya,inda ya zuwa yanzu ya ziyarci kasashen Tajikistan da Maldives kuma nan ba dade wa ba zai isa kasar indiya.(Ibrahim)