Mr. Xi da Madam Park sun ce tattaunawarsu na ranar Alhamis ya yi nasara, sannan suka ce yarjejeniyar da suka cimma zai amfana ma kasashen biyu duka wajen yi masu jagoranci a huldar dangantakarsu.
Shugabannin biyu sun amince cewa, duka bangarorin biyu na da alaka ta hanyoyi da yawa kuma suna amfani da abubuwa da dama iri daya, don haka a cikin sanarwar da aka fitar bayan wannan ganawa, an ce, kasashen biyu sun amince su baiwa junansu isassun dama ganin cewa duka kasashen na da zummar ganin cigaban tattalin arzikinsu da inganta rayuwar al'ummarsu.
Haka kuma shugabannin sun amince sun inganta hanyar sadarwarsu sannan kuma su ci gaba da zurfafa dangantakar hadin gwiwwarsu ta samar da dabaru masu dama ta hanyar da ya shafi yayata aniyar samar da yanayi da ba za'a yi amfani da makaman nukiliya ba a zirin koriya, sannan a mutunta zaman lafiya da kwanciyar hankali mai karko a yankin.(Fatimah Jibril)