in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai bayyana manufar Sin game da kasashen tsakiyar Asiya lokacin ziyara
2013-08-28 14:08:38 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi bayani kan tsarin hulda da kasashen waje na Sin game da kasashen tsakiyar nahiyar Asiya a cikin jawabinsa da zai gabatar lokacin ziyararsa a kasar Kazakhstan.

Mataimakin ministan harkokin kasashen waje na Sin Cheng Guoping wanda ya sanar da hakan a ranar Talata wajen taron manema labarai, ya ce, ziyarar shugaba Xi zuwa kasashen tsakiyar nahiyar Asiya, abin da ya zama na farko tun darewarsa shugabancin kasar Sin yana da matukar amfani.

Shugaba Xi dai zai fara ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan, Turkmenistan, Uzbekistan da kuma Kyrgyzstan tun daga ranar 3 zuwa ranar 13 ga watan Satumba mai zuwa bisa goron gayyatar shugabanni Gurbanguly Berdymukhamedov na Turkmenistan, da Nursultan Nazarbayev na Kazakhstan, Islam Karimov na Uzbekistan, da kuma Almazbek Atambaev na Kyrgyzstan.

A lokacin ziyarar, shugaba Xi zai halarci taro karo na 13 na shugabannin kasashen mambobin hadin gwiwwar kasuwanci na Shanghai a Bishkek, babban birnin kasar Kyrgyzstan a karon shi na farko a matsayin Shugaban kasar Sin.

Haka kuma kamar yadda mataimakin minista na harkokin wajen na kasar Sin Li Baodong ya yi bayani ya ce, shugaban na Sin zai halarci taron shugabanni 8 na kungiyar G20 a St. Petersburg na kasar Rasha daga ranar 5 zuwa ta 6 ga wata bisa gayyatar takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin.

Taron dai na G20 na cigaba da kuma habaka zai mai da hankali ne a kan cigaban tattalin arzikin duniya da daidaito kudade, samar da aikin yi da zuba jari, cigaba da cinikayya.

A lokacin wannan ziyarar, har ila yau, shugaba Xi zai halarci taron kungiyar kasashen BRICS da ya kunshi Sin, Rasha, India, Brazil da kuma Afrika ta Kudu, sannan zai gana da wassu shugabannin kasashen waje da kungiyoyin kasa da kasa.

Sin za ta ci gaba da aiwatar da tsarinta na tattalin arziki mai inganci tare da aiki kafada da kafada da kungiyoyin kasashen duniya domin inganta cigaban tattalin arzikin duniya mai karko da nagarta. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China