A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya buga waya ga takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev don nuna alhini ga mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin tare da jajanyawa iyalansu.
A ranar 17 ga wata da karfe 7 da minti 25 na yamma ne, wani jirgin saman kasar Rasha ya fada yayin da yake kokarin sauka a filin jiragen sama na birnin Kazan dake jamhuriyyar Tatarstan, inda dukkan fasinjoji da ma'aikata 50 dake cikin jirgin sun mutu. (Zainab)