in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci cikakken nazarin game da karfin girgizar kasar Lushan
2013-05-03 20:44:39 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a samu sahihani da cikakken nazari a kan asarar da girgizar kasar Lushan ta haifar, tare da jaddada cewa, sake tsugunar da mazauna wurin da bala'in ya abka mawa zai zama babban aikin da ke gaban masu samar da agaji.

Shugaba Xi yayi wannan bayanin ne a cikin wata takardar umurni da aka fitar a ranar Jumma'ar nan dangane da ayyukan agaji sakamakon girgizar kasar da ta auku mai karfin digiri 7 a yankin Lushan dake lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar a ranar 20 ga watan jiya, abin da ya hallaka mutane kimanin 196 sannan 21 kuma suka bace.

Ya kuma yi kira da a gaggauta fara ayyukan farfado da wuraren da bala'in ya shafa, yana mai nuna bukatar da ke akwai ta fidda tsarin da zai haifar da irin nasarar da aka samu lokacin da bala'in girgizar kasar mai karfin digiri 8 na karkashin kasa ya auku a yankin Wenchuan duk dai a lardin Sichuan a ranar 12 ga watan mayun shekarar 2008.

A cewar Shugaba Xi, tsarin sake ginin ya kasance ya samar da wadatattaun koren filaye wato yalwatattun bishiyoyi da ciyayi don inganta yanayin muhalli da ababen cigaba mai dorewa, tsari na sake gina ababen more rayuwa, ababen bukatun jama'a da kuma gidajen birni da na karkara.

Haka kuma ya yi kira ga jami'an kula da bala'in girgizar kasa da kuma jami'an kula da walwalan al'umma da na tattalin arziki, yana mai cewa a saka duk daukacin sassan da suka hada hada da yanayin zaman al'umma, cigaban masana'antu, ayyukan aikin gona, ababen rage radadin talauci, ayyukan kare birane da muhalli a cikin abin da za'a yi la'akari da su lokacin wannan aiki.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China